Kiwon lafiya

Ko Kunsan Illoli 5 Da Shafe Shafen Da Yan Mata Suke Yake Haifar Musu?

Mata masu yawan son kwalliya ko kun san cewa yawan chaba kwalliya na iya kawo matsalar rashin karfin ido da bata fuskokin ku?

Wasu kwararrun masana kan kwalliyar zamani sun shawarci mata akan rage yin kwalliya kullum domin yana iya bata musu ido da fuskokinsu.

1 – Rashin daukar Ciki ga mace – A nan masaana sun ce yawan irin wadannan shafe-shafe na iya sa mace ta gagara daukar ciki saboda akwai wasu abubuwa acikin man da ke shafawa da ke shiga ta ramukan gashi zuwa cikin jikin mace da kan sa hakan.

2 – Yana kawo tsufa da wuri ga mace – Za ka ga budurwa ta na tsofa haka kawai.

3 – Yana kawo cutar dajin fata, wato ‘Cancer’.

4 – Yawan ciwon kai.

5 – Tsigewar gashi a jiki.

Masanan sun fadi wasu hanyoyi da za a iya bi domin samun kariya daga wannan matsaloli kamar haka;

1 – A rage yawan shafa jan hoda domin yawan shafa shi na kawo kurarraji a huska.

Kamata ya yi a dunga shafa farin hoda.

2 – A daina shafa tozalin zamani wanda wasu ke kira da ‘Gazar’ ko kuma da turanci ‘Eye Liner’ domin yana dauke da sinadarin dake kashe ido. Kamata ya yi a shafa tozalin gargajiya kokuma ‘Kajol’.

3 – A daina amfani da kayan kwalliyan da suka tsufa.

4 – Amfani da gashin idon kanti wato ‘Eye lashi’ na kawo rashin karfin ido domin ana amfani da gam kafin a manna shi kan gashin ido wanda idan an je cirewa ya kan kawo wasu matsaloli kamar kumburin ido, rasa gashin ido, kurarraji da sauran.

5 – A daina amfani da ‘Contact Lense’ domin yana kawo makanta. Contact lense wani abun kwalliya ne da ya yi kama da leda wanda mata kan saka shi a ido domin cansa kalan idon su.