Labarai

Ko Kunsan Garin Da Shugaba Buhari Zeyi Babbar Sallah

Kamar yadda na samu labari cewar yau ne cikin yardar Allah ake tunanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Jagora mai kishin kasar sa da jama’ar sa zai isa Katsina daga nan ya kama hanyar zuwa Mahaifarsa Daura.

Kuma yau ne za muga masu neman gindin zama masu son a gansu a cikin Hotuna tare da Buhari bayan kuma basa kwatanta kadan daga cikin irin halayyar Buhari, Hatta barin jihohin su da suke su bar su kwashi kudin jama’a su yi tafiyar neman suna. mun san cewar Buhari yana tallafatawa gwamnoni kudade su kuma bassa tallafawa kullum sun bar talakawa suna zargin Buhari ya kawo yunwa da talauci to wallahi kuji tsoron Allah.

Kuma daman a wannan gwamnatin tun farko mun fada cewar “Muguwar Kazace Ta Fara Shiga Cikin Akurki” ya kamata a wannan Babbar Sallar A bar ‘yan asalin Daura wadanda suka wahalta suka bayar da gudummawar su a wajen kafa wannan gwamnatin, da su je su gana da shugaban su kar a sake yi musu abun da aka yi musu a “Karamar Sallah” Muna masu rokon Allah ya kai shi lafiya ya kara masa lafiya, Allah yasa a kammala hidimomin Sallah, Amin.

Anas Saminu Ja’en
30/8/2017

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.