Kiwon lafiya

Ko kun san nau’in abincin da ke inganta rayuwar aure?

Inda akwai kwararan hujojji masu bayyana yadda wani takamaimen abinci zai iya bunkasa gamsuwa yayin jima’i, da zai yi kasuwa sosai.

Cin abinci mai kyau da motsa jiki da kuma yawaita tunani mai kyau za su iya inganta rayuwar aurenku. Amma shin gaskiya ne cewa akwai nau’in abincin da za su iya bunkasa rayuwar taku ta aure?

Sinadaran abinci wadanda ke dauke da kwayoyi masu faranta wa mutane rai sun kunshi wasu abubuwan gina jiki masu alaka da bunkasa gamsuwa ko kuma arziki.

Ana tunanin cewa wadanan sinadaran za su iya bunkasa gamsuwa yayin jima’i.

To bari mu duba tarihi ko akwai abin da ke goya wa wadanan ka’idojin baya, sai mu gani ko sinadaran za su iya bunkasa gamsuwa yayin jima’i.

Shin cin kumba (oyster) na aiki?

Kumba (Oyster) kenan mai kama da zuciya cikin wani kwano.

An kiyasta cewa Casanova, wanda ake yi wa lakabi da dan soyayya mafi shahara a tarihi yana cin kumbuna 50 a kullum a matsayin karin kumallo.

Sai dai babu wata tabbatacciyar alaka tsakanin kumbuna da habaka gamsuwa yayin saduwa. To ina wannan labarin ya samo asali?

Masana na cewa lokacin da aka haifi Aphrodite – wato abar bautar soyayya – ta bullo ne daga cikin kumfar ruwan teku… shi yasa ake kiyasta cewa naman ruwa zai iya bunkasa gamsuwa yayin jima’i.

Amma bari mu bai wa masu kaunar kumba wani labari mai dadi, akwai sinadarin zinc a kumba sosai, wato wani abin gina jiki mai habaka sinadarin halittar da namji wato testosterone.

Bincike ya nuna cewa sinadarin zinc zai iya taimakawa wajen magance matsalar rashin haihuwa tsakanin maza da kuma kara yawan maniyyin da namiji ke samarwa.

Ga kuma wasu abubuwan da za a iya samun sinadarin zinc a cikinsu: Akwai jan nama da naman ruwa masu kwanso da ‘ya ‘yan kabewa da gyada da kuma madara.

Shin cakulet mai duhu za ta iya habaka soyayyarku?

Bakin wata mata kenan a lokacin da take shan chakwulet.

Cin cakulet mai duhu zai iya sanyawa ka ji kamar ka fada soyayya a cewar masu bincike, saboda cakulet tana dauke da sinadarin soyayya wato “phenylethylamine” (PEA).

Sinadarin PEA yana yawo a cikin jikin mutum a watannin farko da mutum ya shiga soyayya – yana habaka jin dadi a ran mutum wanda kuma ke da alaka da bangaren nishadin kwakwalwa.

Sai dai sinadarin PEA kadan kawai ake samu a cakulet, kuma har yanzu ba a tabbatar da ko sinadarin na aiki idan an sha cakulet ba.

Ana kuma iya samun sinadarin amino acid tryptophan a koko, wanda ake cewa yana bunkasa gudanar jini da kuma sinadarin serotonin wanda shi ma ke habaka farin ciki.

To amma yaushe aka samu alaka tsakanin cakulet da bunkasa gamsuwa yayin saduwa? Ana ganin cewa ya fara ne a karni na 16.

Hernán Cortés wani sojan karni na 16 dan kasar Sifaniya ne wanda ya jagoranci yaki zuwa cikin Masarautun Maya da Aztec, kuma ya kwace dukkannin yankunan da aka fi sani a Mexico yanzu a karkashin mulkin sarautar Castile.

Ana kuma tunanin cewa shi ne Baturen farko da ya ga cakulet. Ya rubuta wasika zuwa sarkinsa cewa ya ga Masarautar Maya suna shan wani hadin koko wanda ke kara wa jiki karfi kuma yake kore gajiya.

Amma dattijai a Masarautar Castilia sun alakanta amfanin cakulet da wasu abubuwa daban da ‘yan Masautar Maya ba su sani ba su ma, kuma babu wata kwakkwarar hujja mai nuna cewa ana iya amfani da cakulet wurin inganta gamsuwa yayin saduwa.

Ga wasu abubuwan da ake iya samun sinadarin tryptophan cikinsu: kifi da kwai da gyada da alayyahu da kaji da ‘ya’yan itace da kuma abincin da aka samu daga waken suya.

Shin yaji zai iya bunkasa gamsuwa yayin jima’i?

Ataruhu

Dafaffen attaruhu na dauke da sinadarin capsaicin, wanda bincike ya nuna cewa yana samar da sinadarin endorphins (wanda ke samar da jin dadi a cikin jiki).

Sannan kuma yana temakawa wajen sarrafa abinci a jiki kuma ya kara yawan zafin jiki da kuma bugawar zuciya cikin sauri kamar yadda muke ji yayin saduwa da iyali.

Amma kar ku manta da wanke hannayenku bayan amfani da shi!

Shin barasa ko giya tana taimakwa ko kuwa bata harka take?

Mutane biyu suna shan giya

Giya kan taso wa mutum da sha’awa ta hanyar dauke masa kunya, amma kamar yadda tauraron littafin adabin nan na Turanci Macbeth ya fada tana “tana saka wa mutum sha’awa kuma a lokaci guda ta rage masa karfi”.

Sha’awa tsakanin maza da mata kan ragu idan aka sha giya da yawa daga bisani kuma ta dauke wa mutum sha’awar baki daya.

Kuma ma dai warin giya ba zai bar mutum sukuni ba a gado.

Ta yaya za ku kara yawan sha’awarku?

Wata mace a kan gado tana yin jinjina

Bincike ya nuna cewa abinci mai dauke da wasu sinadarai da ake samu daga ganyayyaki yana taimaka wa jikin mutum yayin jima’i, kuma ya magance cutar daukewar sha’awa da ake kira erectile dysfunction (ED).

Binciken ya tabbatar cewa sinadaran anthocyanin, wanda ake samu a dan itaciyar blueberry da kuma wadanda ake samu a itacen citrus, suna magance ED.

Yiwuwar kamuwa da cutar ED tana raguwa da kashi 14% idana ana cin abinci mai dauke da sinadaran da ke cikin ganyayyaki, inda shi kuma motsa jiki ya rage wa da kashi 21%.

Saboda haka, maza ku cika cikinku da kayan marmari!

Wasu masu binciken sun nuna cewa abincin yankin tekun Bahar Rum (Mediterranean Sea) suna bayar da kariya daga ED saboda kusan baki dayansu na ganye ne da ‘ya’yan itatuwa.

Kayan kara karfin sha’awa

Gunkin Aphrodite

Za a iya kasa kayan kara sha’awa na Aphrodisiacs zuwa kashi uku: wadanda suke taimaka wa azzakarin namiji da wadanda ke bayar da karfi yayin jima’i da kuma gamsuwa yayin jima’i.

Sai dai a kimiyyance ba a tabbatar da cewa ko suna aiki a kan dan Adam ba saboda karancin ma’aunin da za a iya auna nasararsu.

Hasali ma, wanda aka tabbatar yana aiki shi ne kanshin ‘ya’yan itatuwa nunannu da kuma rubabbu kuma su ma suna aiki ne kawai ga kwarin da suke cin itatuwan.

Dr Krychman masani ne kan ilimin jima’i. Ya ce mutane suna cin kayan kara karfin sha’awa ne kawai saboda sun yi imanin cewa za su yi masu aiki, sannan ya ce idan abu yana yi maka aiki ai ba sai ka tambayi dalili ba.

Akasarin abin da ake kira kayan kara karfin sha’awa ba su da illa amma ana bayar da shawarar a kauce wa duk wani abu da ba na ‘ya’yan itatuwa ba musamman magungunan komai-da-ruwanka.

Sharadi

Idan kana fama da matsalar daukewar sha’awa da alama kana fama ne da wata cuta. Saboda haka ana so a ko da yaushe a rika tuntubar likita.

About the author

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement