Get New DJ Mixes
Kiwon lafiya

Ko Kasan Yiwa Matarka Kallon Qurilla Na Kara Yawan Shekaru

Wani bincike ya gano cewar ka kurawa matarka idanu na tsawon lokaci yana jinkirta rayuwa.

Binciken na wani masani dan kasar Jamus mai suna Dr. Karen Weathebai ya nuna cewar kurawa matark idanu a kullum yana kawar da hawan jini, ya sanya daidaituwar bugun zuciya da kewayawar jini a cikin jiki.

Yayin binciken da mujallar New England journal of medicine ta wallafa, ta gano cewar likitan yayi amfani da maza magidanta, wanda aka dora akan wannan tsari na tsawon lokaci, kuma aka samu kyakkyawan sakamako.

Sakamakon ya kayyade mintuna 10 a kullum da ake son mutum ya zauna yayi tsai da ransa ya zurawa matar sa idanu, wanda haka dai dai yake da mintuna 30 na wasannin motsa jiki.

Baya ga kara kuzari ga magidanta, likitan yace rayuwa zata jinkirta da kusan shekaru 4, sannan zuciya zata samu lafiya wajen gudanar da aikinta, haka kuma kuma kofofin jini zasu bude domin gudanar da aikin su.