Labarai

Ko Kadan Rashin Kwarewa Ta A Harshen Turanci Ba Ya Damu Na – Hon Gudaji

Dan majalisar wakilan Najeriya, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya shahara wajen tsayawa ya yi magana a zauren majalisar gaba-gadi ba tare ko da yin dar na yin kuskuren harshen turanci da aka saba magana da shi a majalisar ba.

 

A Najeriyar dai an dade ana zargin cewa wasu daga cikin ‘yan majalisa na shakkar tashi su yi magana a zauren majalisar don gudun kada su yi kure, har a yi musu dariya.

Hon. Gudajin ya shaida wa BBC cewa abinda ya ke ba shi karfin guiwar tashi ya yi magana gaba-gadi a majalisar shi ne ya riga ya sa a ransa cewa duk abinda ya ga na gaskiya ne ya kamata ya mike ya yi magana, ko kuma in ya ga wata illa, musamman kan abinda ya shafi talaka.

Game da maganganun da ake yi cewa bai iya turanci ba kuwa dan majalisar Hon.

Kazaure ya ce ai da ma shi ba bature ba ne bahaushe ne Hausa-Fulani.

” Abinda na fahimta shi ne duk lokacin da za ka yi magana a cikin a’umma, duk wata hanya da za ka yi hikima ka isar da sako mutum ya fahimci abinda kake so ya fahimta to ni bukatata ta biya, bana ma tunanin cewa turancina ba daidai bane”

Dan majalisar ya kuma ce dariyar da ‘yan majalisa suke yi a duk lokacin da ya mike zai yi magana ba yana nufin saboda rashin iya turanci na bane, sai dai kawai don suna sha’awar yadda ”nake tashi kai tsaye kuma in basu dariya.”

” Ba dariya ce ta turanci ba, ni kai na in na mike ai tun kan in yi magana ake dariya, idan akwai duk wata damuwa a zauren majalisar sai ka ga da an yi dariyar nan komai sai ya dawo daidai a ci gaba da tattaunawa”.

Sai dai kuma Hon Kazauren yana cikin `yan majalisar da rahotanni ke cewa ba su taba gabatar da kudurin doka ko sau daya a wannan jumhuriyar ba.

Amma kuma ya ce ai ba gabatar da kudiri ne kawai zama cikakken dan majalisa ba, don a lokuta da dama ya kan yi abubuwan da suka fi gabatar da kudirin muhimmanci.

” Ni da nake ganin na zama jagora wajen ganin ko wane kudiri ya zama doka? Tun da sai ka gama kawo kudirin naka ka ga majalisa bata amince ba, sai na tashi na yi magana in ce ya kamata gida ya amince da shi.”

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.