Labarai

Kiyama Ta Kusa Saboda Haka Kowa Ya Shirya – Obasanjo

Kiyama Ta Kusa Saboda Haka Kowa Ya Shirya – Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kowane Kirista ya sake shiri, domin tashin duniya ya matso, kuma kowa ya jira dawowar Yesu Almasihu.

 

Obasanjo ya yi wannan ikirarin ne a ranar Asabar, lokacin da ya ke jawabi a Cocin Afastolika, na garin Igbesa cikin Jihar Ogun.

Ya ce a matsayin sa na dan Adam, ya na son shiga aljanna domin ya kasance tare da mala’iku har su rika wakokin bege tare.

“Kowa ya shirya, domin Yesu Almasihu na kusa ga dawowa.”

Obasanjo ya kara da cewa Allah ba zai gyara Najeriya ba, har sai ‘yan Nijeriya sun tashi sun gyara halayen su kuma sun gyara kasar su.

“Idan za mu fada wa kan mu gaskiya, to kowa ya san akwai dimbin abubuwan da mu ke tafkawa na ba daidai ba a kasar nan.” Cewar Obasanjo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: