Kiwon lafiya

Kiwon lafiya: Me ke sa sauro ya addabi mutum da mugun cizo?

– Mun kawo maku dalilan da su ka sa sauro ke addabar wasu da cizo

– Daga ciki akwai yanayin jinin mutum ko kuma idan ana dauke da ciki

– Zazzabin cizon sauro na kashe Miliyoyin mutane a kowace shekara

Ga dai kadan daga dalilan da su ka sa sauro ke cizon ka kamar yadda Jaridar Punch ta kawo:

1. Yanayin jini

Mafi yawan sauro dai sun fi son cizon masu nau’in jini na ‘O’ a kan sauran irin jinane watau na ajin A, da B, ko AB da sauran su.

2. Juna biyu

Haka kuma wani bincike da aka yi a nan Afrika ya nuna cewa sauro sun fi cizon masu dauke da ciki a kan marasa juna biyun.

3. Jinsin mutum?

Ko ka san cewa macen sauro kadai ke cizo? Haka kuma ta fi son cizon maza ko da mata sun fi wahala idan su ka sha cizon sauron.