Daga Abdullahi Muhammad Maiyama
Babban abun lura a nan shine, a watanninda suka gabata ne kasar Amurka ta aike da sojojinta a kasar Gabon, bayan samun rashin lafiyan bugun zuciya akan hari da wasu mahara suka kaiwa shugaban kasar Ali Bango.
Daga lokacinda ya kamu da bugun zuciyar sai aka garzaya da shugaba Bango zuwa kasar Saudiyya domin neman Magani! Bayan tafiyarsa zuwa kasar ta Saudiyya, sai shugaban Amurka Donal Trump ya aiko da sojojin kasarsa zuwa kasar Gabon domin kiyaye rayukan jama’a akan tashe-tashe hankula….
Bayan aiko da sojin, sai Sarkin Maroko ya aika da goron gayyata inda ya tabbatarda cewa idan aka dawo da shugaba Bango a kasar Moroko zai bashi kariya dakuma haka zaici gaba da Duba lafiyarsa.
Kuma Shugaba Bango Amsa goron gayyatar, inda yanzu haka yake ci gaba da neman magani a kasar Moroko.
Abin mamaki dakuma ban takaici shine yadda wani sojin kasar ta Gabon yayi ikirarin yiwa shugaba Bango juyin mulki, sai dai anyi nasarar dakile wannan juyin mulki da baiyi nasara ba, kuma an kame wasu sojoji hudu da ake zargi da kitsa wannan juyin Mulki…
Sai dai wani abun tsoro dakuma shakku, shine an bayyana cewa yanzu haka ana ganin wasu motocin yaki a babban birnin kasar ta Gabon wato Lebreville….
Kasar Gabon kasa ce mai dinbin arzikin man fetur, wacce take dauke da kabilu, dakuma al’ummomi daban-daban, akwai bukatar masu ruwa da tsaki a kasar ta Gabon su kara zage dantse wurin tabbatarda tsaro a kasarsu, akasin haka kuma idan sukayi wasa lallai wasu bata gari zasuyi Amfani da karfin soji wurin kifarda zaman lafiya a kasar! Tare da kwashe dukkan wasu hanyoyi na ci gaban da kasar ke tunkaho dashi!!! Allah ya kare tsarewa!