Kishin Talaka Da Taimakon Jama`a Ya Sa Mu Ka Nada Atiku Wazirin Adamawa -Lamidon Adamawa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kishin Talaka Da Taimakon Jama’a Ya Sa Mu Ka Nada Atiku Wazirin Adamawa – Lamidon Adamawa

Lamidon Adamawa mai martaba Mustapha Barkindo ya bayyana cewa gudunmuwar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wa jihar Adamawa da kasa Najeriya ba su misaltuwa.

Barkindo ya fadi haka ne da ya ke nada Atiku Abubakar Wazirin Adamawa na bakwai.

” Waziri ba gadon shi ake ba, kowa zai iya zama Waziri. In kira ga sauran sarakunan wannan jiha da su ba sabon waziri duk wani hadin kai davya ke bukata domin samun nasara a wannan sabon matsayi na sa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 662

Shima tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo kira yayi ga Waziri Atiku da ya maida hankali wajen hada kan al’umma.

Wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ministan Abuja, Musa Bello yi wa sabon Waziri fatan alkhairi a matsayin sakon shugaba Buhari.

Cikin wadanda suka halarci wannan buki sun hada da shugaban majalisar wakilai ta tarayya da na dattawa, Dogara Yakubu da Bukola Saraki.

Goodluck Jonathan da Namadi Sambo, sannan da gwamnonin Gombe, Sokoto,Bayelsa da Taraba duk sun halarci wannan buki.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: