Kisan Sojoji: Buhari Ya Fusata Sosai Tare Da Shan Alwashin Kawo Karshen Matsalar

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Kisan Sojoji: Buhari Ya Fusata Sosai Tare Da Shan Alwashin Kawo Karshen Matsalar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa matuka bisa kisan kare dangi da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojin Najeriya a barikin Matele.

Talla

Buhari ya ce wannan abu yayi matukar tada masa da hankali.

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana wa manema labarai matsayar Shugaba Buhari bisa wannan hari.

” Babu wani shugaba a ko ina ne ko yake da zai nade hannu ko ko ya zuba ido ya bari ‘yan ta’adda na kashe masa mutane da sojoji bai kuma dauki mataki ba. Wannan ta’addanci ya tada wa Buhari hankali matuka wanda dole ne a dauki matakin gaggawa domin gano menene yake kawo irin wannan hare-hare bayan irin nasarorin da aka samu a kan Boko Haram.

Talla

” Gwamnati zata maida hankali wajen ganin ta samar wa dakarun ta makamai masu nagarta domin samun nasara kan wadannan ‘yan ta’adda.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

” Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin ci gaba da kokari kamar yadda gwamnati ta ke yi a da wajen samun galabar Boko Haram yanzu, sannan ya roki ‘yan siyasa da su daimaida abin siyasa cewa wannan abu ne da ya shi kowa da kowa dan kasa.

Idan ba a manta ba daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele, karamar hukumar Guzamala jihar Barno ya bayyana wa manema labarai cewa shima Allah ne yasa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Najeriya da ke aiki a wannan bariki basu sha da dadi ba.

Ko da yake tun kafin wannan hari, sai da Boko Haram suka aika wa Sojojin sakon cewa zasu kawo farmaki barikin. Ba nan ba kawai har da wasu dake Kauyukan Barno.

” Boko Haram sun far wa barikin mu ne ranar litini da misalin karfe 6 na yamma.

” A lokacin da sojan da ke can kololin sama wato mai hangen nesa daga barikin ya sanar mana cewa ga fa gungun mayakan Boko Haram nan sun kunno kai zuwa wannan bariki sai dukkan mu muka daura damara muka ja daga muna jiran su.

” Gaba daya batakashin bai dauke mu tsawon mintuna 45 ba domin mayakan Boko Haram din

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: