Kisan Da Akayiwa `Yar Uwata Ban Yi Bakin Ciki Ba, Murna Nayi Mata -Sanata Marafa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sanatan ya bayyana hakan ne a yayin zantawar da yayi da manema labarai jim kadan bayan kammala Jana’izarta da sauran bayin Allah da aka kashe a Munmunan harin da aka kai a Zamfara.

Sanata Marafa ya cigaba da cewar, kisan da akayi wa ‘yar uwar tashi Shahada tayi, kuma a magana ta gaskiya hankalin shi ya kwanta maimakon ace an sace ta ne ba’a san inda take ba, kuma a tsarin Musulunci duk wanda aka kashe bisa ga zalunci yayi shahada ne, inda yayi Addu’ar Allah ya jikan ‘yar uwar tashi da sauran wadanda aka kashe a Jihar ta Zamfara, sannan yayi addu’a Allah ya kubutar da Mijinta wanda ‘yan Bindigar suka sace.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta…

1 of 661

Sanatan ya kuma bayyana cewar, Bala’in dake faruwa a Zamfara ya zama ruwan dare inda ya shafi Gidan kowa, an wayi gari a yau Bala’in yazo gidan shi, kuma da yardar Allah wannan Bala’in zai yi naso ya fada gidajen ainihin wadanda ke da hannu wajen kawo fitinar a Jihar Zamfara.

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: