Kiristocin Jihar Kaduna Ba Zasu Zabe Ni Ba Koda Na Dauko Fafaroma Ne a Matsayin Mataimaki -El-Rufa`i
Gwamnan jihar kaduna Nasir El-Fufa’i yace yasan kiristocin jihar Kaduna ba zasu zabe shi ba koda ya dauko fafaroma ne a matsayin mataimakinsa
Gwamnan ya fadi hakan ne yau alhamis 17 ga watan junairu a wani shirin siyasa da gidan talbijin na channels take gabatarwa.
El-Rufa’i yace ” dauko Hadiza Balarabe musulma a matsayin mataimakiyar sa da yayi a zabe mai zuwa ya janyo kace nace kala kala kuma hakan ya faru ne saboda wannan bakon al’amari ne a siyasar jihar Kaduna. Ya zabo ta ne saboda ta chanchanta kuma yana da yakinin lashe zaben da ke tafe ranar 2 watan maris