Daga Ibrahim Rabiu Kurna
Assalamu Alaikum
Mai girma sabon kwamashinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Muhammad Wakili cikin girmamawa muna so kasan babbar matsalar mu anan jihar Kano ita ce matsalar daba da bangar siyasa wanda gurbatattun yan siyasa suke amfani dasu domin cimma wata manufar su.
Alhamdulillah
Kamar yadda tsohon kakakin rundunar yansandan Jihar Kano, SP Magaji Musa Majia ya fada a baya cewa anan Jihar Kano ba muda matsalar tsaro ta Boko Haram, garkuwa da mutane, fashi da makami da fadan kabilanci duk Allah ya kare mu.
Tabbas kalaman tsohon PPRO haka suke ga duk wanda ya kwana ya tashi a Jihar Kano yasan haka.
Muna godiya da wannan taimako da Allah yai mana ba wayon mu bane balle iyawar mu kariyar Allah ce.
Allah ya taimake ka ya hadaka da mashawarta da mataimaka nagari wajen ganin a magance wannan matsala ta daba da bangar siyasa.
Muna kara yi maka fatan alkairi, Allah ya taya ka ruko.
Amin.
#Rariya