Wata likitan yara Juliet Ochi ta yi kira ga uwaye da ma’aikatan kiwon lafiya da su guji yin amfani da sabulun da ke kau da cutar fata da ake kira ‘Medicated Soap’ wajen wanke gaban mata.
Wata likitan yara Juliet Ochi ta yi kira ga uwaye da ma’aikatan kiwon lafiya da su guji yin amfani da sabulun da ke kau da cutar fata da ake kira ‘Medicated Soap’ wajen wanke gaban mata.
Juliet ta ce yin hakan na kashe wasu kwayoyin ‘Bacteria’ wanda ke kare al’auran mace daga kamuwa da cutuka da kan yi wa gaban mace lahani
” Tun farko anyi wannan sabulun ne domin kawar da cutukan dake kama fatar mutum ne amma ba don wanke al’auran mace ba.”
Ta ce kamata ya yi a dunga amfani da sabulun da ake kira ‘Toilet Soap’ domin banda tsaftace gaban mace da sabulun keyi zai kuma kare ababen dake samar da kariya ga al’auran mace.
Add Comment