Labarai

Kila nan gaba kyaftin ne kawai zai rika magana da lafiri

A wasan kwallon kafa ba kamar na zari-ruga-ba (Rugby), babu dokar da ta hana dan wasa magana da lafiri
Kyaftin zai kasance dan wasa daya kawai da yake da ikon magana da alkalin wasa a kan wani babban abu a yayin wasan kwallon kafa, idan har aka amince da wasu shawarwari a Birtaniya.
A ranar Juma’a ne hukumomin wasan kwallon kafa hudu na Tarayyar Birtaniya – Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa, hadi da Fifa, karkashin hukumar da ake kira Ifab, za su tattauna akan wasu sauye-sauye da ake shirin bullo da su a wasan na kwallon kafa, a Birtaniya, da suka hada da wannan doka ta hana duk wani dan wasa magana da alkalin wasa in ba kyaftin ba.
Taron wanda za a yi a filin wasa na Wembley, hukumomin da suka hadu suka yi Ifab din ne ke gudanar da shi a duk shekara. 
Darektan wasanni na hukumar ta Ifab, David Elleray ya ce, ya kamata a ce kyaftin din kungiyar kwallon kafa ya wuce dan wasan da zai sanya wani abu kawai a hannunsa, ya ci a ce yana da iko sosai.
Elleray wanda tsohon alkalin wasan Premier ne ya ce, matakin zai kawo karshen yadda ‘yan wasa kan zagaye ko su rufar wa alkalin wasa, idan wni abu ya faru, ko ya yi wani hukunci.
Darektan ya ce tuni sun tattauna a kan matakin, inda suka nemi shawarwari daga kwararrun ‘yan wasa da koci-koci da alakalna wasa, kuma da dama sun amince da shirin.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.