Uncategorized

Kickstarter ya dauki wani dan jarida aiki

Shafin intanet na Kickstater ya dauki wani dan jarida aiki da ya dorawa alhakingano dalilin da ya sa shirinsa na karaminjirgin sama marasa matuki bai yi nasara ba duk da yawan tallafin da aka ware wa shirin.Mutane dubu goma sha biyu suka samarda kudi sama da fam miliyan biyu domin gudanar da shirin da aka yi wa lakabi da Zano amma duk da haka shirin bai yi tasiri ba.,Ana dai sa ran dan jaridar Mark Hariss zai fadakar da masu zuba jari da kuma jama’a a kan gazawar kamfanin .Kamfanin Torquing da aka dorawa alhakin aiwatar da shirin ya dakatar da shirin a watan Nuwamba ba ta re da cikaalkaurukan da ya yi ba.Mr Harris ya ce kamfanin Kickstater ya dora masa alhakin gano abin da faru tun farkoda aka kaddammar da shirin zuwa yanzu domin masu goyan shirin su samu bayyanan da suke bukata kakashin matsayar da suka cimma da kamfanin.