Kannywood

Ki Karewa Maryam Yahaya Kallo Sai Ki Dauki Darasi

Daga Fulani Shuaibu
Na ƙarewa masanaantar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kallo da nazari ƙarshe na gane cewar ana neman kudi kuma ana samun su sai dai sanaar bata isa ta samarwa Jarumai masu tasowa duniyar da yan mata masanaantar suke da ita hannu ba, maana irin yadda suke fantamawa da manyan Motoci da kudi da gasar gina gidaje da kuma baje kolin sanya kayayyaki na alfarma saboda haduwa a wajen biki ko taro.

A saboda haka ne na kalli jaruma mai tasowa Umme Rahab, nake ganin ya kamata in ce wani abu ta iya yiwuwa hakan ya zamewa iyayen ta da saura masu kula da ita ko waɗanda hakkin tarbiyya ta ya rataya a kan su izina.

Jarumar ta fara da tauraro mai haske kuma tana da dunbin masoya kamar yadda kuke gani a shafin ta na yanar gizo, jarumar ta sami karbuwa a wajen mutane, duniyar kannywood tana gara mata yadda ya kamata, to amma hakan ne daidai a irin wannan lokacin a irin yarinya mai ƙuruciya kamar ta?

Ina kira da Umme Rahab, ta karewa rayuwar Jaruma Maryam Yahaya kallo kuma tayi nazarin rayuwar ta a masanaantar Kannywood zuwa yau da nake wannan rubutun.

Bazan ce Maryam Yahaya ta gama shirin Fim ba amma zai yi wuya ta dawo yadda ya kamata, Maryam ta ce zazzabi cizon sauro da taifod ne abun dake damun ta amma duniya basu yarda ba kamar yadda ita ta san karya take yi labarin rashin lafiyar ta abun a tausaya mata ne kuma muna addua Allah ya bata lafiya.

Dan Allah Ummi, kada ki bari rayuwar Yan mata Kannywood ta zame miki jiki, gasar hawar manyan Motoci, gina gidaje,riƙe manyan Wayoyi da sauran su, zaki yi duk abun da kike so amma waɗanda zasu yi miki wannan hidimar baza su bar ki yadda suka same ki ba, kiyi ƙokarin amfani da ƙuruciyar ki wajen gina gobe mai kyau.

Ƙasa da kashi 15% cikin 100% ne suke iya kiran jaruma Maryam Yahaya a waya bare har suyi ƙokarin zuwa gidan su dubiya bare har a yi tunanin dorewar zumunci, haka masanaantar take.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: