Kazafin da aka yi min kan Maryam Yahaya yasa na daina Social Media

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Biyo bayan labaran karya da aka wallafa kan jarumi Tanimu Akawu, ya yanke shawarar daina duk mu’amala da duk wasu shafukann sada zumunta , domin kuwa a cewar sa labaran karya sunyi yawa, saboda haka ya daina duk wani abu da yake da alaka da Social Media, ciki kuwa hadda su Facebook, Instagram, Twitter da sauran su.

Tanimu Akawu

Idan ba a manta ba a shekarun baya wani labari ya fantsama a shafukan sada zumunta da aka ruwaito cewa wai Tanimu Akawu yace matan Kannywood yawancin su karruwai ne, duba da yadda yarinya za ta zo cikin ‘yan kwanaki ta mallaki babbar mota gida da waya mai tsada, su kuma da suka shafe shekara da shekaru babu abinda suka tsinana.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 404

A rahoton kuma an bayyana cewa jarumin ya bada misali da Hadiza Gabon da Maryam Yahaya da irin motoci da wayoyin da suke rikewa.

Sai dai bayan labarin ya karade shafukan sadarwa, Tanimu Akawu ya fito ya musanta wannan batu, inda yake cewa wannan magana ba daga wurin shi ta fito ba, karyace aka sharara masa, jarumin har yayi yunkurin daukar matakin shari’a kan wadanda suka shirya masa wannan labari na karya, inda yace shi babu gidan jaridar da yayi hira da su akan wannan lamari, duk kuwa da cewa wasu na ganin zancen da aka ce ya fada gaskiyane.

Sai dai a wata ‘yar takaitacciyar hira da aka yi da jarumin da kafar yada labarai ta DW Hausa, an jiyo jarumin na bayyana alhininn sa na wannan labarin karya har ya zuwa inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin dalilin sa na daina duk wasu shafukan sada zumunta na zamani.

Ga dai yadda hirar ta su ta kasance:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.