-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Kaya Ba Za Su Yi Arha Ba, Amma Tattalin Najeriya Zai Mike –Gwamnan CBN


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnan Babban bankin Najeriya na CBN watau Godwin Emefiele yace za a cigaba da fama da tsadar kaya a Najeriya har zuwa tsakiyar shekara mai zuwa.

Sai dai Gwamnan yace duk da hakan abubuwa su na mikewa a Kasar.

Alkaluman tattalin arziki sun nuna cewa za a cigaba da fuskantar tsadar farashin kaya a Najeriya har zuwa cikin shekarar 2019.

Yanzu dai alkaluma sun nuna cewa ana fama da hauhawan farashin kayan masarufi ne da maki 11.4% a Najeriya.

Babban bankin Kasa na CBN ya tabbatar da cewa duk da haka dai tattalin arzikin kasar ya kama hanyar mikewa kuma CBN din zai cigaba da sakin makudan Daloli a kasuwa domin hana Dalar Amurka yin raga-raga da darajar kudin kasar na Naira.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Jimillar arzikin Najeriya na GDP zai cigaba da bunkasa a shekarar nan a dalilin cigaban da ake samu a bangaren noma da sauran su.

Tattalin arzikin kasar zai kara zabura daga karshen bana zuwa shekarar 2019 saboda kudin da za a kashe a zaben da zaayi.

Yanzu haka dai Gwamnatin Buhari ta hana shigo da wasu kaya har 41 cikin Najeriya. Wannan ya taimaka wajen habaka harkar noman shinkafa da sauran hatsi.

Masana harkar tattali dai sun rage burin da suka sa na cigaban da za a samu bana a Duniya.

Bayan wannan rahoto na Jaridar The Sun, kwanaki kun ji cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP na Shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi alkawarin gyara tattalin Najeriya idan ya samu mulkin kasar nan a 2019.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: