Kawar Da Boko Haram Amurka za ta sayar wa Nigeria jiragen yaki
Rahotanni sun ce kasar Amurka ta amince da wata yarjejeniya wadda za ta sayarwa Najeriya jiragen yaki na kimanin dala miliyan 600 domin taimaka mata a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da majalisar dokokin kasar shirin gwamantin kasar na amince da sayar da jiragen ranar Laraba.
Lamarin da ya soma kwanaki 30 na duba kan yarjejeniyar a lokacin da ‘yan majalisar kasar ke da damar hana cinikin.
A karshen mulkin tsohon Shugaba Barack Obama ne aka dakatar da yajejeniyar bayan wani jirgin yakin Najeriya ya yi lugudan wuta kan wani sansani ‘yan gudun hijira.
Rahotanni sun ce fiye da mutum 200 harin ya kashe.
Amman a yanzu karkashin Donld Trump, wanda ya ce yana son ya kara abubuwan da Amurka ke sayarwa.
Amnesty International ta zargi sojin Najeriya da kaddamar da kisan gilla kan dubban masu tada kayar baya.
Amman babu wani sojan da aka gurfanar kan zarge-zargen.
Idan aka ci gaba da cinikin jiragen, sojin Najeriya za ta yi maraba da shi domin ta dade tana kuka kan rashin isassun makaman yaki.
Add Comment