Labarai

Kasar Nijeriya Na Fuskantar Zaman Lafiya, Cewar Ministan Tsaro

Daga Abubakar A. Adam Babankyauta
Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce kasar nan na fuskantar zaman lafiya duk da irin kalubelen tsaro da take ciki.

Rundunar sojin kasar nan sun kasance suna yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sama da shekaru 10.

The Cable ta ruwaito cewa, dakarun suna cigaba da gwagwarmaya da ‘yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan.

A yayin karbar kwamitin majalisar dattawa a kan lamarin tsaro a ranar Talata, ya ce an kashe jami’an tsaro a wasu wurare amma duk da haka rundunar sojin kasar nan ta samu nasara.

“Najeriya tana fama da matsalar tsaron cikin gida sakamakon addabar da mayakan Boko Haram suka yi a arewa maso gabas da kuma ‘yan bindiga a jihohin Niger, Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara,” yace.

“Wadannan kalubalen sun matuukar zama dalilan da suka sa muke rasa zakakuran dakarunmu dake kan aiki.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: