Mawaki kuma jarumi Abdullahi Muhammed Katsina wanda akafi sani da Abdu Boda ya sami lambar yabo da kyautar karramawa akasar sudan, wannan shine karo na uku da aka karrama mawakin, a wannan shekarar ma kasar sudan ta karrama Abdu Boda Katsina bisa gogewarsa afagen waka mai dauke da amana da nishadantarwa.
A wannan watan na Ramadan Kareem wannan jarumin mawaki ya karbo lambar girmamawa akasar sudan, wanda an tara manyan mawakan kasar da daraktocin kasar da masu fada aji na kasar.
Abdu Boda yace: ya yi murna wanda bai taba yin irinta ba tunda yazo duniya, domin acewarsa yanda yaga manyan mutane sun taru domin sa sai hawayen murna suka soma kwaranya a idanunsa.
Tabbas, Abdu Boda ya zama raina kama kaga gayya. domin ba wanda ya taba tsammanin sudan zasu karrama Abdu Boda, amma kuma sai ya zama har sau uku suna karrama shi sabida fasaharsa.
Wasu masoyan Abdu Boda sunyi walima acikin garin katsina sabida wannan karramawa da akayiwa gwaninsu.
Add Comment