Labarai

KAROTA: Hukumar Karota Ta Kori Ma’aikacin Daya Fasa Tayar Babbar Mota a Kano

advertisement

Hukumar lura da cunkoson ababen hawa a jihar Kano KAROTA ta sallami wani jami’in ta guda bayan ya fasa tayar babbar mota.

Hukumar ta kori Jamilu Gambo biyo bayan rashin iya aiki da hukumar ta ce ya nuna bayan sun sami saɓani da direban babbar mota.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar K/Na’isa ya sanya wa hannu, ya ce korar jami’in ya biyo bayan zaman gaggawa da shugaban hukumar ya yi da kwamishinan ƴan sanda.

Ya ce baragurbin jami’in nasu ya fasa tayar babbar motar ne a snaadin sa ‘in sa da ta kaure tsakanin su da direban motar.

Ya ƙara da cewa a sakamakon fasa tayar motar sauran masu manyan motoci su ka tare babbar hanyar Kano zuwa Hadejia.

Shugaban hukumar Karota Baffa Babba Ɗan’agundi ya gode wa ƙungiyar NARTO a bisa gaggawar shiga tsakani tare da samar da masalaha.

Sannan hukumar ta nemi afuwar al’umma musamman waɗanɗa su ka sami tsaiko a sakamakon toshe babbar hanyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button