Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa babu wani aikin tattara sakamakon zabe da zai gudana a babban dakin taro na ICC da ke Abuja, har sai karfe 6 daidai na yammacin yau Lahadi, hukumar ta shaida cewa kafin lokacin fara tattara sakamakon zaben daga jihohi, tana shirye don magance duk wasu matsaloli da ka iya tasowa.
A farko hukumar ta sanar da cewa karfe 10 na safiyar yau Lahadi za ta fara tattara sakamakon, amma saboda magance wasu matsaloli da ka iya tasowa sai hukumar ta dage aikin tattara sakamakon zaben daga jihohi zuwa karfe 6 na yammacin yau din, zuwa yanzu dai ana sa ran kusan dukkan jihohin da aka gudanar da zaben sun fara tattara nasu sakamakon wanda shi zasu kawo dakin taron ICC din.
#leadership