Vitamin A magani ne dake da matukar mahimmanci wajen kara girman jikin yara kanana wanda rashinsa kan iya sa yaro ya kamu da cututtuka daban-daban.
Sai da abin takaici ne da aka gano cewa wasu asibitocin gwamnati na fama da karanci wannan maganin.
Gidan jaridan ‘Leadership Weekend’ ta gudanar da bincike inda aka gano cewa asibitocin gwamnati kamar cibiyar kiwon lafiya dake Dutse, asibitin Bwari, cibiyar kiwon lafiyar dake Wuse Zone 3, asibitin Garki da cibiyyar kiwon lafiya dake Area 2 na matukar fama da karancin maganin.
Binciken ya kara nuna cewa asibitocin gwamnati kamar hakan na jira na dan wani lokaci kamar na tsawon watanni shida kafin su sami wannan maganin sannan bayan sun samu asibitocin na bada maganin na tsawon kwanaki biyar ne kawai a mako.
Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya na Abuja Mathew Ashikeni ya ce an sami akasi akan hakan ne saboda rashin horo kan iya tattalin amfani da magungunan da wasu asibitocin basu da shi.
Ya ce saboda hakan ne gwamanti ta fito da dabaran samar wa asibitocin dake karkashin ta da wannan magunguna sau biyu a shekara ko kuma bayan duk watanni shida.
Wani ma’aikacin asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya wanda bai so a fadi sunan sa ya ce dabaran da gwamnatin Najeriya ta dauka ya yi daidai sannan hakan bai saba wa dokokin kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ba wanda ya ce ‘’kamata ya yi yara kanana su sami maganin ‘Vitamin A’ bayan watanni shida da haihuwa.”
Add Comment