__¥__
Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya tabbatar da cewa karamin guda guda daya ne kacal ya mallaka a yankin Karu da ke cikin Babban birnin tarayya Abuja.
Magu ya yi wannan ikirarin ne a kotu inda maka jaridar ” The Sun” kotu bisa Wani rahoto da ta wallafa kansa na cewa ya mallaki gidaje biyu na alfarma a yankin da attijirai ke zama a cikin Abuja wato, Yankin Maitama.
- Advertisement -
Shugaban EFCC ya shaidawa kotu cewa wannan rahoton ya bata masa suna a idon duniya don haka ya nemi kamfanin jaridar ya biya shi diyya tare da neman afuwa kan wannan rahoton.