Labarai

Karamar Hukumar Sabuwa Dake Jihar Katsina, Ta Zama Mafakar ‘Yan Bindiga

…Kungiyar “Arewa Media Writers” Tana Kira Ga Gwamnatin Jihar Katsina, Da Shugabannin Tsaro Dasu Dauki Matakin Gaggawa Akan Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Addabi Al’ummar Karamar Hukumar Da Sauran Yankunan Dake Fama Da Matsalar Rashin Tsaro

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

A zantawa da kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” tayi da wani mazaunin yankin mai suna Jamilu Tela Sayau, ya shaidama kungiyar cewa a kowace rana ta Allah sai ‘yan ta’adda sun shigo garuruwan Sabuwa, Sayau, Dungun Mu’azu, Tashar bawa, Galadima, sun kashe mutane, sun kwashi dabbobi, sun fasa shagunan mutane sun kwace wayoyin jama’a tare da yin garkuwa da mutane, don neman kudin fansa.

Haka zalika ya kara dacewa ko’a ranar Talatar da ta gabata 4- ga watan Feb, 2020, saida ‘yan bindiga suka kawo wani mummunar hari a garin Sabuwa, inda suka yima mutum 13 kisan gilla suka tafi da shanun wani mutun mai amalanken dibar yashi.

Al’ummar wannan yanki a halin da ake ciki yanzu hankalinsu ba kwance yake ba tashe yake, saboda a kullum mata da kananan yara basu iya barci a cikin gidajensu sai a wajen gari da saman bishiyoyi, sakamakon yadda ‘yan ta’adda suke cin karensu ba babbaka.

A karshe kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” na kara Kira da jan hankali ga Gwamnati da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki dasu gaggauta daukar matakin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin Arewa gaba daya.

Fatan kungiyar “Arewa Media Writers” taga yankin Arewa ya zauna lafiya, dama kasar Nijeriya baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: