Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar TY Buratai ya sanar a ranar Talata cewa ya amince da karin girma ga sojoji 6,199 da ke aiki da runduna ta musamman, Lafiya Dole, wadda ke yaki da kungiyar Boko Haram.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan watsa labarai na runduna ta bakawai ta sojin kasar Laftanar Kanar Kingsley Samuel ya fitar ta ce Laftanar-Janar Buratai ya taya sojojin murnar sabbin mukaman nasu.
Ya umarce su da su kara azama wajen fafutikar da ake yi ta yaki da Boko Haram, a arewa maso gabashin kasar.
Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ta Lafiya Dole, tare da wasu ‘yan kato da gora suka kama wasu ‘yan Boko Haram hudu a kayukan Kurnari da Nayinawa da ke wajen garin Damaturu a jihar Yobe.
Mutanen da aka tabbatar cewa ‘yan Boko Haram din ne sun hada da Bukar Waziri, mai shekaru 25, da Mammade Lawan dan shekara 20, haka kuma an samu wani yaro, Isah Muhammadu, mai shekara 15 da mahaifinsa Muhammadu Damina, mai shekara 40, da suka fito daga Talala.
Binciken farko ya gano cewa sun tsere ne daga wata maboyarsu da ke Talala da Buk da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno, saboda yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu.
Rundunar ta Lafiya Dole ta kara zafafa yunkuri na dakile masu harin kunar bakin wake a jihar Bornon Najeriya, inda sojojin yankin suka sha yin nasara kan sama da mata ‘yan kunar bakin wake takwas, da Boko Haram suka aiko domin tarwatsa al’ummar da basu ji ba basu gani ba.
Sojojin rundunar Lafiya Dole na aiki ne da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, domin dakile maharan kunar bakin wake.
Sanarwar ta jaddadawa al’ummar Najeriya cewa su rika sa ido sosai, kuma su tabbatar sun yi shaida wa hukuma duk wani abu da suka gani da bai kwanta masu ba.
Bbchausa
Add Comment