Sheik Isiyaka Rabi’u Zai Samar Da Jami’ar Mahaddata Kur’ani
Khalifa Isyaka Rabiu (Khadimul Kur’an), babban dan kasuwa kuma mahaifi ga Abdulsamad mai kamfanin BUA ya yi yinkurin samar da sabuwar jami’a a jihar Kano mai suna AT-TANZEEL UNIVERSITY.
Wacce za ta mayar da hankali wajen samar da dalibai mahaddata Alkurani mai tsaki.
Shirye-shiryen kaddamar da makarantar sun yi nisa inda nan gaba kadan za a yi bukin bude ta tare da fara karatun dalibai a makarantar.
Al’ummar musulmai suna godiya. Allah ya kara mana irinku masu yawa a cikin al’umma.
Add Comment