Labarai

Kano: Kwankwaso ya kauracewa taron jam’iyyar APC a Kano

Sanata Kwankwaso ya kauracewa taron jam’iyyar mai mulki ta APC shiyar jihar Kano

– Ana sa ran za a yi zaben sabbin kwamitin zartarwa na jam’iyyar a taron

– An gabatar da mutane 15 ba tare da wata hamayya ba don cika gurbin ofisoshi 15 na jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kauracewa taron jam’iyyar mai mulki ta APC shiyar Kano wanda ake gudanar a halin yanzu a Kano.

Taron, wanda ake gudanar a cikin zauren filin wasa na Sani Abacha, ta samu halartar gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje da ‘yan majalisar jihohi da na tarayya da wasu jigon ‘yan siyasa da kuma shugabannin jam’iyyar don zaben sabbin kwamitin zartarwa na jam’iyyar a jihar.

Kwankwaso da Ganduje

Kamar yadda Arewablog ke da labari, Kwankwaso, wanda yake yanzu sanata, ya kasance a kafar wando da gwamna Ganduje a kan jagorancin jam’iyyar APC a jihar Kano. Ganduje shi ne mataimakin gwamnan ga Kwankwaso har karshen watan Mayu 2015 lokacin da ya bar ofis a matsayin gwamna jihar.

 

A zaman taron jam’iyyar a jihar, mutane 15 masu biyayya ga gwamna Ganduje aka gabatar ba tare da wata hamayya ba don cika gurbin wasu matsayi 15 a kwamitin sashen zartarwa na jama’iyyar.

Mutanen sun hada mukaddashin shugaban jam’iyyar na yanzu, Abdullahi Abbas a matsayin anihin shugaban jam’iyyar. mataimakinsa, Shehu Maigari da kuma sakataren jam’iyyar na yanzu, Ibrahim Sarina.