JARUMA ZAINAB INDOMIE TA MAYAR DA MARTANI GA WASU JARUMAI.
Jaruma Zainab Indomie tasha jinya a kwana-kwanan nan, amma Allah cikin ikonsa yanzu ta sami sauki ta warke gaba daya harma ta mayar da jiki.
Alokacin da Zainab Indomie bata da lafiya jarumai maza da mata kowa yana fadan albarkacin bakinsa akan rashin lafiyar Zainab Indomie.
Acikin wasu jaruman cewa suke yi kanjamau (AIDS) Zainab ta jajibowa kanta.
Wasu kuma cewa suke yi asirin sababbin jarumai mata suka yi mata. To, Zainab Indomie ta mayar da martani bayan da ta warke, acewar Zainab, Duk wanda yace na jajibo kanjamau ko mace ko namiji tsakanina da shi ko ita Allah ya isa. domin rashin lafiyar da nayi saukakace daga Allah.
Add Comment