Kannywood

Kannywood: Yadda Tallar Fim Din 'Gwaska Return' Ya Zo Da Sabon Salo

Shahararren jarumin finafinan Hausan nan Adam A. Zango ya zo da sabon salo na tallar finafinai ta kafafun sadarwa, wadanda suka hada da Facebook, Twitter, Instagram da sauransu.
 
Kusan wannnan shine karo na farko da aka soma sanya tallar fim a kafar sadarwa, inda a baya an fi mayar da hankali wajen sanya tallar finafinan a cikin sabbin finafinan da za su fito.
Da yawa daga ciki masu bibiyar harkar finafinan Hausa da ma sharhi kan masana’antar fim har da wasu ‘yan fim, sun yaba da sabon salon tallar fim din da jarumi Adam Zango ya fito da shi.
Mubarak Umar wanda aka fi sai da Mubarak Khan, wanda kuma yana daya daga cikin masu fashin baki a masana’antar fim, ya bayyana lamarin a matsayin wani sabon ci gaba da jarumi Adam A. Zango ya fito da shi wanda zai taimakawa ‘yan fim wajen tallata hajarsu.
…masu karatu za su iya kallon tallar fim din a nan.
DOWNLOAD TRAILER HERE
 
Source In Rariya