Kannywood

Kannywood: 'Satar fasaha na matukar illata sana'armu'

Ali Nuhu ya ce nuna fim din Mansoor a sinima ya hana masu satar fasaha cin karensu babu babbaka

Masu ruwa da tsaki a fagen fina-finan Kannywood sun dade suna kokawa kan batun satar fasaha da suka ce tana kassara sana’arsu, to ko yaushe za a kawo karshen wannan halayyar ta bera?

Satar fasaha wata hanya ce ta ci da gumin wani ko wasu. A takaice, satar fasaha na nufin sace wani aiki da mutum ya yi: ko a rubutu ko a fina-finai da dai sauransu, inda barayin kan kwafi ko wallafa littafi ko fim su sayar da su ba tare da izinin mutumin da ya samar da su ba.
Wani abu na baya-bayan nan da ya fito da satar fasaha da irin illar da take yi a Najeriya shi ne kan littafin da fitaccen marubucin nan kuma dan jarida Olusegun Adeniyi ya rubuta mai suna “Against The Run of Play”.
Kafin ma a kaddamar da littafin, wanda aka yi ta sa ran karanta shi saboda irin batutuwan da ya tabo a siyasance, masu satar fasaha sun kwafe shi sannan suka rika rabawa ta hanyar kwanfyuta, lamarin da ya yi matukar tabawa marubucin rai.
Da yake bayani kan batun, Mr Adeniyi ya ce abin takaici kan masu satar fasaha shi ne yadda abin da suke yi ke kashe gwiwar masu shirya finan-finai.
Da alama wannan batu nasa haka yake domin kuwa a Kannywood, satar fasaha ta kashe gwiwar mutane da dama wadanda kusan a iya cewa ba su da na biyu a wurin hada fim.
 
Mallam Aminu Saira, wani fitaccen mai hada fim ne wanda ya kwashe shekara da shekaru yana fito da manyan fina-finai.
Sai dai ya taba shaida min cewa yadda satar fasaha ta zama ruwan-dare ta sa gwiwarsa ta yi sanyi sosai.
“Mun yi ta fafutikar hana wadannan barayin fasaha amma abin ya ci tura. Za ka ga furodusa ya kashe miliyoyin kudi wurin shirya fim amma yana fito da shi barayin fasaha za su je su kwafe shi su rika sayarwa. Maimakon mutum ya samu riba sai faduwa zai kirga”, in ji Mallam Aminu Saira.
Shi ma Mallam Falalu Dorayi, fitaccen furodusa kuma jarumi a Kannywood, ya gaya min kwanakin baya cewa sun sha kama barayin fasaha sai dai hakan bai yi tasiri sosai wajen magance matsalar ba.
A cewarsa, “An sha kira na garuruwa da dama inda aka ga barayin fasaha kuma mu kan je mu kama su mu mikawa hukumomi amma babu matakin da ake dauka. Hakan yana kashe mana gwiwa.”
A farkon shigowar gwamnatin Muhammadu Buhari masu sana’ar shirya fim sun kai masa ziyara inda ya sha alwashin magance matsalar amma babu wani mataki na zahiri da aka dauka domin magance matsalar.
‘An samu mafita’
Sai dai da alama matakin da masu shirya fina-finan suka dauka na soma nuna su a sinima zai kawo karshe ko kuma ya rage satar fasaha.

A wata hira da BBC, jarumi Ali Nuhu, wanda ya fito da sabon fin dinsa mai suna Mansoor, kuma ya nuna shi a sinima kafin sayar da shi a faifan VCD, ya ce “matakin zai rage irin barnar da masu satar fasaha ke sa wa muna yi”.
“Sau da dama za ka ga furodusa ya kashe miliyoyin kudi wajen hada fim amma da zarar ya fito da shi sai barayin fasaha su kwafe shi su rika sayarwa ba tare da ya samu ribar da yake bukata ba; hasalima faduwa muke yi.”
A nasa bangaren, Falalu Dorayi ya ce sun kwashe shekara uku suna neman mafita ga satar fasaha, yana mai cewa matakin da aka dauka na nuna fina-finai a sinima zai sa su daina tafka asara.
“Mun dauki tsawon lokaci muna yin kira ga hukumomi su kare mu daga masu satar fasaha amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, don haka ne muka yanke shawara daukar wannan mataki.
“Abin da zai ba ka haushi shi ne yadda furodusa zai kashe makudan kudi wajen hada fim amma da ya kai wa ‘yan kasuwa sai su ce ya bar musu a matsayin bashi; kuma idan ya bar musu suka soma sayarwa sai barayin fasaha su sace fim din su rika sanya shi a YouTube. Mu mun tashi a banza kenan”, a cewar Falalu Dorayi.
Sai dai Mallam Aminu Saira ya ce ko da yake nuna fina-finai a sinima na da matukar muhimmanci, amma ba hakan ne kadai zai yi maganin satar fahasa ba.

Mr Adeniyi ya ce ya samu riba duk da sace fasahar da aka yi na littafinsa ya samu riba.
A cewarsa, “Wannan mataki ba zai magance masu satar fahasa ba domin kuwa idan ka duba za ka ga cewa sinimomin da muke da su ba su da yawa. Sinima biyar ce da mu a cikin Shoprite da ke birnin Kano, kuma masu kallon da za su shiga ba su wuce cikin cokali ba idan ka yi la’akari da dumbin masu kallon da muke da su.
“A duk wata ana fitar da fim fiye da 20, kuma masu shiga sinima ba su wuce kashi daya cikin dari ba. Akwai bukatar hukumomi su sanya hannu a gina sinimomi da gidajen kallo kafin wannan mataki ya yi amfani.”
Ya kara da cewa suna daukar matakin bude shagon kallon fim na intanet mai suna Hausa Empire ta yadda mutum zai yi rijista kafin a ba shi damar shiga ya kalli fina-finai, kamar dai yadda sauran bangarorin fina-finan duniya ke amfani da Netflix.
Amma Mallam Falalu Dorayi ya ce nan gaba kadan za su fadada wannan mataki inda za su rika shiga lungu da sako na karkara domin nuna fina-finan a gidajen kallo.
A nata bangaren, jaruma Rahama Sadau, wacce fim dinta na Rariya na cikin wadanda aka nuna a sinima, ta shaida min cewa da zarar ta mayar da kudinta za ta soma fitar da fim din a faifan DVD domin mutanen da ba su da sukunin zuwa sinima su saya.
Masu sharhi a Kannywood dai sun ce matakin nuna fina-finan a sinima zai kawo karshen wa-ka-ci-ka-tashin da ake yi wa masu kashe kudinsu suna yin fim amma barayin fasaha su sace.
Sai dai sun ce dole ne gwamnati ta sanya hannu wurin bai wa masu shirya fina-finai tallafin da za su bude karin sinima da gidajen kallo domin nuna su.
 
Souce IN BBCHAUSA

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.