Kannywood

Kannywood Mattarace Ta Fitsararru Wayanda Suka Kwashe..

Daga Abdurrahman Abubakar Sada
Babu yadda za’a yi ƴa mace ta kwashe kayan ta daga gidan iyayenta ta koma gidan KANNYWOOD, sannan ta yi ƙarshe mai kyau.

Kai ko aikin Hajji da yake wajibi daga wajiban musulunci, shari’ar Musulunci bata yadda ƴa mace ta niƙi gari zuwa aikin Hajji ba, sai tare da muharraminta. To ballantana masa’antar KANNYWOOD da babu abinda ake karantarwa sai fasiƙanci da alfasha.

Babu yadda za’a yi ƴa macen da ta tare kannywood tayi ƙarshe mai kyau, sai dai wata rahama ta Allah.

Don haka, ku kalli rayuwar ƴan Kannywood matattun su da rayayyun su, wacece ta yi ƙarshen ƙwarai?

Don haka muna ba ku shawara ku masu sauran sauran sutura ta mutunci a kannywood, Kuji tsoron Allah, tun kafin abinda ya samu na gabaninku ya same ku.

Allah Ya ƙara shiryar da mu bakiɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: