Kannywood

Kannywood: Ko Meye Dalilinta Na Cewa Aure Lokaci Ne – Hadiza Gabon

– Hadiza Gabon ta yi bayani game da auren ta

– Hadiza Gabon ta ce shi aure lokaci ne

– Jarumar tace ita kanta yazu neman mijin take yi ido rufe

Fitacciyar jarumar Kannywood kuma kyakkyawa a fuska da jiki mai suna Hadiza Gabon ta yi karin haske game da masu yi mata nasiha da shagube akan wai taki tayi aure.

 

Jarumar bayan da maganganun suka je kunnen ta sai ta kada baki tace: “Shi aure lokaci ne kuma nufi ne na Allah, amma babu wata mace da zata yi fatan kaiwa kamar ni ba tare da tayi aure ba, kuma hankalin ta ya kwanta”

AREWABLOG.com ta samu labarin cewa Hadiza Gabon din ta kuma ci gaba da cewa: “Saboda haka nima ina fata kuma ina adduar Allah ya kawo min miji nagari na samu nima in zama amarya.”

Indai ba’a manta ba a kwanan baya ne tsohuwar fitacciyar jarumar ta Kannywood watau Safiya Musa ta fito tana mai bada shawarar cewa ya kamata yan matan fim din suyi aure.

 

Souce In Naij.com

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.