Abdulamart Mai Kwashewa – Shahararren Kamfanin shirya Fina-finan Hausar nan, Wanda ya Saba Kawo muku Fina-Finai ingantattu, ma su ma’aina, Ilmantarwa da kuma nishadantarwa: ABNUR ENTERTAINMENT Wannan kamfani mai suna a sama ya na gayyatar ilahirin al’umma musamman mata, zuwa taron tantancewa [Audition] Wanda za a yi domin fitar da jaruman da za su taka rawa [role] a Sabon Kasurgumin shirin da za su ga barar kwanan nan mai taken MAI KYAU! [Roles] din da za a taka rawa sun hada da:
1:BILKISU Ana bukatar wadda za ta taka rawar BILKISU ta kasance;
a- shekaru 20_23
b- Kyakkyawar gaske, doguwa, mai sassanyar murya, mai yanayi na ban tausayi, ta iya Hausa karbabbiya, wadda za ta iya Karatu da kuma rubuta.
2: NADIYA Ana bukatar wadda za ta taka rawar NADIYA ta kasance;
a- Shekaru 20_25
b- Kyakkyawa mai cika idanu, mai tattausar murya, matsakaiciya a fagen tsayi da kiba.
3: AMINU:
a- shekaru 25
b- Matsakaici a fagen tsawo da kauri, mai yanayin ban tausayi, mai nutsuwa da kamala, mai ilmin zamani da na addini. Za a gabatar da wannan tantancewa ranar:
Date: 30 ga wannan wata.
Wuri: Social Welfare, Court Road.
Add Comment