Kannywood

Kannywood: Akwai Rashin Wayewa A Industry – Sani Danja

Jarumi Kuma Mawaki Sani Danja yace akwai rashin wayewa acikin industiri. yayi wannan bayani ne acikin hirar da akayi da shi acikin Mujalla Fim ta wannan watan.

Acewar Sani Danja:
.
Tabbas, akwai karanchi dama rashin wayewa acikin industiri, domin yawan hawa motoci da yawan saka sababbin kaya masu karin guga bashi ne yake nuna akwai wayayyu a industiri ba.

Ita wayewa tana nufin sani akan al’amura daban-daban bawai saka kaya masu kyau ba, saka kaya masu kyau tsafta yake nufi ba wayewa ba.

Da yawan jaruman da suke industiri basu da hadin kai, domin basu waye da amfani gamida mahimmancin hadin kai ba. kowa idan ya shigo industiri buri yake yafi dan uwansa suna da tarin kudi a kannywood. tabbas, wannan tsantsar rashin wayewane. akasashen da suka ci gaba kuma suka waye ba haka suke gudanar da harkar fim ba. haduwa suke suyi aiki tare su gudu tare su tsira tare .(harmony). amma mu ba haka bane a industiri. inji Sani Danja.

 

Write Sani Ciroma

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.