
Hadiza Gabon ta taba lashe kyautar jarumar jarumai
Jarumar, wacce ta wallafa wani dogon sharhi a shafinta na Instagram, ta yi zargin cewa mutane suna jifan su da maganganun da ba su dace ba, don kawai su ‘yan fim ne.
A cewarta, “Ina mamakin yadda mutane suke shiga abin da babu ruwansu. Baka aikawa mutum goron gayyata ba sai ka gan shi a profile[shafinka]. Ka ji wai har yana fada maka yadda za ka yi rayuwa.
“Na san dai kai mai bayar da shawara dan fim ya yi kaza, ko ya yi kaza kai ba Ma’asumi ba ne. Akwai abubuwa da dama da kake ba daidai ba. Me ya sa baka gyara naka ba?.
Hadiza Gabon ta ce masoyan mutum suna ba shi shawara ne, ba wai su zage shi ba.
Ta yi shagube ga masu zaginsu, tana mai cewa ” Kai mai gulma idan ba za ka iya ganin[abin da muke yi] ba, ka kawar da idonka”.
Jarumar dai ta yi fice wajen fitowa a manyan fina-finai, kuma ana yi mata kallon daya daga cikin wadanda suka fi kame kansu a cikin masu yin fina-finan Kannywood.
Add Comment