Kanfanin Google Zai Ba ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Damar Anfani Da WiFi Kyauta

2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Reshen Kamfanin Google dake Nijeriya ya sanar da cewar, yana shirin bai wa ‘yan kasar miliyan goma da suka fito daga garuruwa biyar damar yin amfani da kafar internet ta Wi-Fi.

Acewar Kamfanin, Wi-Fi 200  na Google dake a cikin tashoshi dake garuruwan biyar da suka hada da, Legas, Kaduna Fatakwal, Ibadan da Abuja, zasu amfana ne a shekarar  2019.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 23

Daraktan Kamfanin a Nijeriya Juliet Ehimuan-Chiazo ce ta sanar da Haldane a jawabin ta a lokacin kaddamar da tashoshin, ta yi nuni da cewa shirin zai kuma bayar da dama wajen yin amfani da Data a cikin sauki  Acewar Juliet Ehimuan-Chiazor, yin amfani da Wi-Fi din kyauta an sanya a cikin hadaka ta internet a cikin karni na 21 da daya kuma kamfanin kofar sa a bude take wajen yin hadaka da sauran  masu harka a fannin.

Acewar sa, daya daga cikin kalubalen shi ne “mun gano cewar samun kutswa a cikin  Data ya yi karanci kuma ba ‘a samun ta a wadace kuma a cikin sauki wanda munyi amamanar samar da ita a wadace zata inganta tattalin arzikin kasar zamu kuma samar kaddamar da ita ta hanyar yin hadaka.”

Ta ci gaba da cewa, “zamu fara da Legas tare da garuruwa hudu kuma a shirye muke mu fadada shirin zuwa 200 a garuruwa hudu a kasar nan a shekarar 2019. Shima a nashi jawabin akan shirin mataimakin sashen kaya na kamfanin Anjali Joshi yace, shirin zai karade sauran kasashen dake cikin nahiyar Afirka

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.