Labarai

Kamfanonin Sadarwa Da Ke Nijeriya Zasu Dakatar Da Whatsapp Da Skype

Kamfanonin sadarwa na waya da ke Nijeriya na neman hanyar magance damuwan asarar kudaden shiga da su ke samu a kirar kasashen waje da mutane ke yi.
Suna so su cimma manufar su na samun naira triliyan 20 na kudaden shiga, suna ganin za su iya samun nasaran haka idan suka tare mutane daga samun daman shiga Skype da sauran sabis da su ka shafi kira ta yanar gizo.
Mutane ma su biyan kudi domin samun irin wadannan sabis din|
ana ganin ƙila za’a hana su amfani da wadannan ayyukar kamar kiran murya da bidiyo a kan WhatsApp da kuma Facebook.
Kamfanonin Sadarwa suna cewa al’amurran da suka shafi ayyuka da Skype wanda za’a iya sanya mutum ya karba kira daqa sabis tarhon gargajiya. Kira ga masu amfani da sabis din Skype ba’a cajin ko sisi, yayin da kira zuwa ga tarho na gargajiya farashin na zuwa a sauki, ana cajin kudi ta wani hanya inda mutum zai saka kudi ta wani tsari mai amfani lambar asusun ajiyansa na banki ya cire kudi ya saka zuwa ga asusun sa na Skype kafin ya samu damar kiran lambobin tarho na gargajiya (debit-based user account system).
Karin Yunƙuri da aka samu na masu samar da hanyoyin kira ta murya da kuma sakonnin waya kamar ta hanyar Whatsapp, Blackberry da Viber na cinye cannikin kudaden shiga Nijeriya na harkokin kamfanonin sadarwa da ke kasar 

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.