Bayan da uwar kamfanin Etisalat da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shelar janye sunanta daga Najeriya, hukumar da ke sa ido kan harkar sadarwa a kasar (NCC) ta amince da sauya sunan Etisalat Nigeria zuwa 9Mobile.
Kamfanin ya ce duk da cewar sunansa ya sauya, nagartar aikin da ya ke wa masu hulda da shi bai sauya ba.
Kamfanin ya ce ya zabi 9Mobile ne domin ci gaba da tasirinsa na kasancewa kamfanin sadarwa na hudu mafi girma a Najeriya.
Uwar kamfanin Etisalat ya janye ne daga Najeriya domin kamfanin ya kasa biyan bashin da gamayyar bankunan kasar 13 ke binsa.
Da bankunan suka yi barazar kwace Etisalat Nigeria, sai hukumar NCC da babban bankin Najeriya suka shiga tsakani domin kare ayyukan mutane sama da 4,000 da kuma harkar kudin Najeriya.
Ita dai uwar kamfanin ta Eitsalat ta janye jarinta daga reshenta na Najeriya ne bayan ta ga rikicin da kamfanin ya shiga.
Bayan Hukumar NCC da babban bankin Najeriya (CBN) suka dauki matakin sake fasalin kamfanin ne, uwar kamfanin ta Etisalat ta janye sunanta daga kasar.
Add Comment