Labarai

An Kama Wani Mutum Da Katin ATM Guda 848 A Filin Jirgin Sama

An Kama Wani Mutum Da Katin ATM Guda 848 A Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano

Wani da ake zargin dan damfara ne mai suna Yasir Salihu Abdullahi ya shiga hannun hukuma a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano dake jihar Kano bayan an gano katin ATM guda 848 a wurinsa.

An kama Yasir ne dai a daidai lokacin da yake shirin shillawa kasar Dubai ta jirgin Misra.

 

Majiyarmu ta ‘Daily Nigerian’ ta rawaito cewa katin ATM din na dauke da na bankin GTbank guda 490, na Access Bank guda 289 yayin da sauran kuma na bankunan kasar nan daban-daban ne.

Yanzu haka dai an mika shi hannun hukumar EFCC domin ci gudanar da bincike a kansa.

Rahotanni sun nuna cewa a watan Disamba na shekarar 2015, wani dan shekaru 29 mai suna Yahaya Saifullahi shi ma an kama shi da katin ATM guda 870 da wasu na’urar cirar kudi guda biyu a filin jirgin na Malam Aminu Kano.

 

Souce In Rariya