Labarai

An kama wani mawaki kan yin rawar dab

An kama wani sanannen mawaki a Saudiyya saboda yin rawar dab yayin wani taron rawa da waka a a kudu maso yammacin kasar.

Abdallah Al Shahani, wani mai gabatar da shiri a talbijin, jarumin fina-finai, kuma dan asalin kasar Saudiyya, ya yi rawar ne wacce ake rufe goshi a dan rankwafa a yayin wani taron wakoki da aka yi a birnin Taif cikin karshen makon da ya gabata.

An haramta rawar dab a kasar, saboda hukumomi na ganin ta a matsayin wata al’ada ta masu shan kaye maye.

Bidiyon rawar dab da Mista Al Shahani ya yi ya bazu ne a kafofin sadarwa na zamani, kuma dubban mutane sun yi ta yada batun a shafin Twitter.

Abdallah Al Shahani lokacin da yake rawar dab a Taif, da ke Saudiyya a makon jiya

An yi amannar cewa rawar dab ta samo asali ne a birnin Atlanta na Georgia da ke Amurka, kusan shekara biyu da suka gabata, amma an samu masu son rawar matuka a duniya ne bayan da shahararrun mutane da manyan ‘yan wasa da ‘yan siyasa kamar su Hillary Clinton suka fara yin irin rawar a wajen taruka.

A baya-bayan nan ne hukumar da ke yaki da masu shan kwaya ta ma’aikatar cikin gida ta Saudiyya ta haramta yin rawar, saboda ana ganin tana da alaka da masu shan kayen maye sosai.

Ma’aikatar ta wallafa wata takarda ta sanar da sako da ke gargadin mutane a kan illar da yin rawar dab ke da shi kan matasa da al’umma, kuma ta hana kwaikwayonta.

Hukumomin Saudiyya sun haramta rawar dab

Ba a dai tabbatar da ko dama Mista Al Shahani ya shirya yin rawar ko kuma dadin sha’ani ne kawai ya dauki hankalinsa har ya yi ta a lokacin ba.

Sai dai mawakin ya nemi afuwa a shafin Twitter ranar Talata da safe, inda ya rubuta cewa, “Ina neman afuwar gwamnatinmu mai daraja da kuma masu bibiyata kan rawar da na yi ta dab a wajen taron mawaka na Taif. Don Allah a gafarce ni.”

Matakin Mista Al Shahani dai ya raba kan masu bibiyar shafukan sada zumunta.

Da yake magana kan muryoyin mata da ake iya jiyowa a bidiyon da Mista Al Shahani ya yi wasan, wani dan jarida Ayed Al Ayed, da ya rubuta a Twitter cewa: “‘Yan mata, har yanzu ina jin ihunku, kuma abin na damuna. Duk wanda ya karya doka za a kama shi. Godiya ga jami’an tsaro.

Wani ma @brakalhmede ya sake rubuta cewa, “Wannan abu ya yi muguwar illa kan mutane. Duk da bayanin da ya yi gaskiya ba za mu yarda ba.”

Singer Abdallah Al ShahaniABDALLAH AL SHAHANI
Mawaki Abdallah Al Shahani

Sai dai wasu na ganin yin hakan ba laifi ba ne.

“Na tabbata kuskure aka samu, don na san mutumin nan sosai, yana da kyawawan dabi’u, kuma tun da ya nemi afuwa, kuma ya ce ba da niyya ya yi hakan ba,” in ji wani mai gabatar da shiri a talbijin @Kemmooalharbi.

Sai dai ba wannan ne karo na farko da wani mawaki ya yi rawar dab ba a Saudiyya.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce wani mawaki Rabeh Sager ma ya sha yin rawar dab a wuraren taruka.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement