-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

KAMA SHARIFF NASTURA ASHIR ZALUNCI NE -Aliyu Sani Madaki


1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shariff Nastura Ashir sanannan dan gwagwarmaya kuma shugaban kungiyoyin hadaka ta kungiyoyin Arewa sanan mai kokari wajen kwato hankin talakawa kuma ba’a sanshi da shiga harka ta’addanci ba.

Kundin tsarin mulki na kasa section 40 ya bawa dukkan dan kasa damar yin zanga zanga cikin lumana kamar yadda 2011 mutane da dama harda wasu gwabnoni ayau suka maida Wuse 2,Abuja wajen zanga zanga kuma domin rashin yarda da karin kudin petrol.Haka ma,2014 shugaban kasa na yau,Shugaba Muhammadu Buhari ya shugabanci sauran manyan yan adawa sukayi zanga zanga don nuna rashin jin da dinsu na kashe mutane sabo da matsalar Boko Haram.Kuma sanin kowane cewa gwabnati ta wannan lokaci bata kama kowa ba duk da cewa an rufe garin Abuja na kwana da kwanaki.

Masu mulki ayau su sani(power is transient)Mulki na Allah ne,yau gare ka,gobe ga wanin ka.Kuma a wancen lokacin Shugaba Jonathan zai iya kama shugaban yanzu amma Don shi Democrat baiyi haka ba.Kundin tsarin mulki na kasa ya bamu damar zanga zanga Kuma akwai hukuncin manya kotuna na kasa da yace,yan sanda basu da damar suce sai sun bada izini sannan za’ayi zanga zanga.

Kundin tsarin Mulki ya bawa dukkan dan kasa damar fadin albarkacin bakin sa a section 39,sannan section 40 ya bawa duk dan kasa damar zanga zanga cikin lumanata.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Ayau NIgeria muna gwabnatin siyace ba 1984 sanda muka nunawa duniya rashin sanin hakki da mutunci dan Adam.

Kama Sharif Nastura Ashir cin mutuncin sane kuma da tauye masa hakki ne,na dan kasa.Muna kira da babbar murya cewa asake shi,kuma bawa dukkan yan kasa damar su kamar yadda kudin tsarin mulki ya bamu.

Asani mu yan Arewa ba,bayin wani bani kuma tsoran kowa akan hakkin mu da mutuncin mu da addinin mu.Kuma kama mu akulle, bazai hana mu neman yancinmu ba.

ASAKI SHARIFF DA GAGGAWA,ADAINA ZULUNCI
AKAWO KARSHEN KASHE KASHE A AREWA DA KASATA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1 Comment
  1. Anonymous says

    Your Comment

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: