Labarai

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Su 40 A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

An kara kama masu garkuwa da mutane su 40 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Rundunar yan sandan Nigeria ta sake gabatar da karin wasu mutane 40 da ake zargi da garkuwa da mutane su karbi kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kakakin yan sanda, CSP Jimoh Moshood yace a yayin simamen da suka kai mabuyan masu garkuwan sun kuma kubutar da mutane Uku wadanda akayi garkuwa dasu.

Sannan yace sun gano makamai da suka hada da Bindigogi kala-kala da albarusai da sauransu. Yace sun kuma samu Laptop da Ipad da wayoyin hannu da Gwala-gwalai da sauran dukiyoyi wadanda barayin suka kwace a hannun mutane.

 

Hausa times ta ruwaito kakakin yan sandan ya kuma ce sun kai simame mabuyan barayin dake Rijanah a hanyar Abuja zuwa Kaduna da sauran wajaje a cikin dazuzzukan.

A makon da ya gabata ne dai rundunar yan sandan ta gabatar da wasu mutane 32 yan fashi da makami da masu satar mutane da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja

Jimoh ya bayyanawa Hausa times sunayen wadanda aka kamo din kamar haka:- Ali Bello (gang leader), Goma Shehu, Mohammed Muju’a, Danladi Hassan, Mohammed Abubakar , Daniel Owobi, Egwu Ogiri, Bashir Haruna , Shedrach Hosiah, Victor Yohanna , Suleiman Isah.

Akwai kuma Abbas Aliyu, Bala Isiya, Hafiz Jibrin, Aminu Mohammed, Abdullahi Adamu, Tukur Ado, Iliyasu Soda, Mohammed Musa, Aliyu Halilu, Ali Adamu, Ahmadu Ya’u, Shehu Habu, Ishakwu Ibrahim da Mustafa Ibrahim

Sauran sun hada da Tanko Abdullahi, Jibrin Mohammed, Jibrin Wali, Tijjani Ahmad, Mohammadu Rabiu, Suleiman Mohammed, Dahiru Bello, Abdulkarim Bello, Mohammed Abubakar, Usman Abdullahi, Umar Garba, Abdulrahaman Amadu, Mu’ázu Salisu, Bala Isiyaku da Mohammad Sani.

Mista Mashood yace mutanen da ake zargin sun amsa laifukansu saboda haka nan bada jimawa ba za’a gurfanar dasu gaban kotu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.