An Kama Bayahuden Da Ya Yi Badda Bami Yana Limanci

22

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jami’an kasar Libya sun sanar da cewa mutumin da suka kama a matsayin kwamandan kungiyar Da’esh, yana aiki ne da kungiyar leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne ta Mosad.

Tashar telbijin din al-jadid ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa; limamin masallacin mai suna “Abu Hafs” an kama shi ne a garin Banighazi da ke gabacin kasar Libya.

 

Binciken da aka gudanar akan shi ya tabbatar da cewa mutumin bayahude ne dan haramtacciyar kasar Isra’ila kuma sunanshi na gaskiya shi ne; Benyamin Afrahim.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

Jami’an gwamnatin kasar ta Libya sun tabbatar da cewa; Afraham yana a karkashin rundunar leken asiri da ake kira “Masu kama da larabawa’ da ke karkashin Mosad, aikinsu kuwa shi ne yin leken asiri a cikin kasashen larabawa.

Afraham ya shiga kungiyar Da’esh, har ta kai shi ga zama kwamanda da mayaka 200 a karkashinsa, kafin daga baya ya zama limamin masallaci a Banighazi.

Rahotanni sun nuna cewa aga cikin manufofinsa shi ne bude yaki a cikin kasar Masar.

 

Source In Rariya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.