-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Kalubale Ga Sojojin Najeriya


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kalubale Ga Sojojin Najeriya

Daga Ammar Muhammad Rajab

Abin da yasa nake tausayawa jami’an tsaron ‘kasarmu, Soja da ‘Yan Sanda shi ne: ana zaluntarsu ba su san ana zaluntarsu.

Tun a wurin Tirenin (musamman Soja), ake nuna masa ba shi da wani ma’kiyi illa farar hula. Shiyasa ma idan abu ya hada ka da Soja, ko rigima ce ‘personal’ tsakaninka da shi, zaka ji yana ce maka: “wannan ‘bloody civilian’ zai rena ni.”

Da yawansu zaka ga ba wanda suke zalunta sai farar hula.

Su ci kayansa, su take hakkinsa. Su zalunci mutum yana gani, sai dai ya yi Allah ya isa. Duk wannan muna gani akan idonmu ke aukuwa.

A kasuwa ne, a Unguwa ne, a layin ATM ne, a makaranta ne, balle kuma Uwa-Uba cikin Barikinsu. Shi Soja ma daga cikin ‘Orientation’ din da aka yi masa akwai ‘Obey before complain’, komai sai dai ka bi, babu saka hankali a ciki ko tunani, ko da kuwa abin da aka umurcesa hauka ne tsagwaro a cikinsa.

A haka aka tarbiyyantar da Sojojinmu. Shiyasa a tarihin Sojan Nijeriya kaf, farar hula ‘yan ‘kasarsa ya fi kashewa fiye da kowa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 14

- Advertisement -

Da gaske ban ji dadin yadda ake kashe Sojoji a ‘kasarnan sa sunan wata ‘kungiya wai ita ‘BOKO HARAM’, saboda abin da na yi imani da shi shi ne: ba wata kungiya Boko Haram, karyar tsiya ce kawai.

Domin ko da ganin irin kisan da ake yiwa Sojojinmu, da yadda Sojojin ke ranta ana Kare idan su ji tawagar wadanda ake ce ma Boko Haram sun taho, ka san mutane ne wadanda aka horas suka kuma san yadda Sojojin kasarmu suke, sune ke zuwa su kashe su.

Gaskiya lokaci ya yi, da ya kamata Sojojin ‘kasarmu da ‘yan Sandan ‘kasarmu su rika saka hankali a ayyukansu, su gane manyan ma’kiyansu sune: masu tura su a kashe su. Farar hula ba makiyinsu bane ko kadan.

Su gane cewa: manya-manyansu da suke zaune a Hedikwata a Abuja, ba za su so wasan kwaikwayon BOKO HARAM ta kare ba. Saboda suna amfana da rashin tsaron a kasarnan.

Domin su ake fitarwa da makudan kudade da sunan su samar da tsaro.

To idan suka samar da tsaron wa zai kara fitar musu da wannan kudaden?

-AMMAR MUH

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: