Kalubale Biyar Da Kasuwancin Intanet Ke Fuskanta A Nahiyar Afrika

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A yayin da ake yiwa nahiyar Afirika kallon tattalin arzikinta na iya farfadowa musamman idan ta rungumi kasuwancin intanet, sai dai duk da rungumar wannan fannin da wadansu suka yi, kafafen Intanet da suka shahara a bangaren huldar kasuwanci ake kuma hulda da su a nahiyar ba su da yawa. Nahiyar Afirika ta kasance daya daga cikin nahiyoyin duniya da suka rungumi fasahar kasuwanci ta shafukan intanet. Ana ganin masu sana’o’in dogaro na amfana da wadannan hanyoyi wajen tallata hajojinsu tare da bunkasa tattalin arzikin nahiyar ta Afirika. Domin a kasashen da su ci gaba tuni wannan sabuwar tsari na kasuwancin Intanet ya yi zarra, domin tsarin wanda kimiyya da fasaha ya samar da shi, dimbin masu sana’o’in dogaro da kai ne suka yi masa kwamba domin ganin sun yi amfani da dabarbaru irin na kasuwanci wajen samun kwastamomi cikinsa domin su rika siyan hajarsu da suke tallatawa. Hakazalika kamfanunnuka ma ba a barsu a baya ba wajen amfana da wannan tsari ta hanyar tallata hajarsu tare da samun dimbin riba mai gwabi. Duk da irin ci gaba da sauki da wannan fasahar kasuwancin Intanet ke da shi, amma al’ummar Afirika suna da fuskantar gagarumin matsala da irin wannan kasuwanci. Domin har yanzu da yawan al’umma ba su iya baiwa wannan hanya muhimmancin da za su iya siyan kayan biyan bukatarsu ta wurin ba. Amma ana ganin cewa idan har masu ruwa da tsaki akan harkokin kasuwanci a nahiyar Afirika suka baiwa wannan bangare muhimmanci, to za su fito da hanyoyin da za su iya magance matsalolin da ake fuskanta wadanda ke sanya shakku da fargaba a zukatan mutane har suke nesantar huldar kasuwanci ta hanyar Intanet. Wannan dalilan ya sa a wannan mako, a shafinmu na Kimiyya ya bijiro da wadansu kalubale da marubuncin yake ganin sune babban matsalolin da ya sanya al’umma ba su rungumi siyan kayayyakin biyan bukatunsu ta Intanet.
1- Kalubale na farko shi ne akwai rashin yarda: Mafi yawan mutanen Afirika har yanzu suna da tsoron siyan abu a shafin Intanet sakamakon samun labarurruka da ke nuni da yadda ake yin karo da masu zambo cikin aminci. Misali; wadansu ba su da amincin su sanya bayanan abin da ya shafi asusun ajiyar bankinsu a shafin Intanet gudun ka da su fada hannun macuta. A yayin da masu ilimi kan sha’anin huldar kasuwancin Intanet suke gudun ka da ‘yan dandatse su wawushe musu kudi idan sun yi kutse a irin wadannan shafin. Wannan dalilin da ma saura ya sanya ya zama dole masu kasuwancin Intanet su samarwa da shafukansu da suke huldar kasuwanci da su tsaro na musamman wanda zai baiwa mutum amincin hulda da su. Ko kuma su samar da hanyarnan ta mafi sauki ta sai an kawo min kayayyakin da na siya ta intanet har inda nake sannan na biya. Wannan zai yi magance wannan kalubale na farko.

2-Tsadar Amfani da Intanet: Wani kalubale na biyu kuma da ake fuskanta a nahiyar Afirika, shi ne tsadar amfani da shafukan Intanet. Ta yadda mutum ba zai iya amfani da shafukan Intanet ba sai ya siya abin da ake ce ma ‘DATA’ a turance, wanda za ka iya siyansa ko a ‘mega bytes’ ko ‘giga bytes.’ Sannan siyan wannan ‘DATA’ din ba shi da sauki a nahiyar Afirika. Misali; a Nijeriya idan kana amfani da layin MTN, ba za ka iya samun ‘1 giga bytes’ ba akan kudi naira dari 500, sai kana tsarin ‘MTN Pulse.’ Idan ko ba haka ba, kudin zaka gay a zarce. Wannan yasa wadansu suke ganin ba za su tsaya batawa kansu lokaci suna shiga shafukan da ake siyar da kayayyakin biyan bukatu a Intanet alhali duk za su iya samun su a shaguna garin su ko ma Unguwarsu. Wannan ya nuna ke nan, idan har ana son a magance wannan matsalar, wajibi ne gwamnati ta sanya hannunta a ciki wajen rage tsadar amfani da Intanet din, ta hanyar tilastawa kamfanunnukan da suke da alhaki wajen samar da wannan ‘DATA’ din, domin su rage kudin siyansu a baki daya nahiyar Afirika.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

SHIN KUNSAN ‘YAN 419 SUN FI YAWA A HARKAR KASUWANCIN…

1 of 20

3-Yadda ake turo da kayan: Matsala ta uku da yake shafar kasuwancin Intanet shi ne matsalar da ake fuskanta wajen turo wa da wanda ya siya kayan sakonsa. Matsalar karancin akwatun karbar sakonni da ake da su a Afirika yana kara dagula al’amarin kasuwancin Intanet. Inda ake samun wadansu akwatun sam ba su aiki, wadansu kuma suna aiki, amma ana fuskantar matsaloli da su. Shiyasa wadansu shafukan kasuwancin Intanet din sun fi maida hankali a kan amfani da motoci ko mashina wajen aikowa da mutum kayansa, wanda wannan ke sanya kayan su kara tsada. Domin magance wannan matsalar, ya zame wajibi wadanda suke samar da shafukan huldar kasuwanci, su samar da hanya mafi sauki da za ta rika saukakawa wajen aikowa da karbar wadannan kayayyakin.

4-Bambancin Harshe Da Kabila: Harshe na da matukar muhimmanci a kasuwancinmu na yau da kullum. Domin sai an fahimci abin da kake tallatawa sannan za a siya. Wannan ke nan yana daya daga cikin kalubalen kasuwancin Intanet. Domin mafi yawan shafukan huldar kasuwancin Intanet, zaka same su cikin harshen turanci ake tallata hajar da ake son a siya. Kuma nahiyar Afirika nahiya ce da take da bambance-bambance harshe, da kabilu, sannan ga bambancin tsarin tafiyar da tattalin arziki da siyasa. Wannan yasa wadansu shafukan kasuwanci na Intanet suke fuskantar matsaloli wajen aiko da kayyyakin da ake siya a wurinsu daga wata kasa zuwa wata kasa, domin sai sun biya musu haraji. Domin rage wannan matsalar yana da kyau, masu irin wannan kasuwancin, su samar da hanyar huldar kasuwanci da mutanen da suke yankinsu ne kawai, domin saukakawa da kuma rage fuskantar matsala.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: