Kalaman Nura M Inuwa Masu Jan Hankali Ga Matasa

7

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shararren mawaki nura m inuwa yayi jan hankali musamman ga matasa na wannan lokacin namu masu biyewa harkar siyasa amma kullin wahalar da rayuwarsu ake an kuma kasa canza wannan wahalar da ake fama da ita.

Mawakin Nura M Inuwa Yace:-

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Ina Makomar Dalibai 101 Da Jarumi Adam A. Zango Ya Yi…

1 of 331

Abun tunani da tambaya shine kowa ya fito so yake a zabeshi, shin babu wani wanda ya fahimci dan siyasa da zai tsayawa talaka?

Naso ace akwai wani dan gwagwarmaya daya da zai tsaya ya jajirce ya shige gaba wajan wayar da kan Al’umma su san matsayin masu neman matsayin a gurinsu,

Inda hali ma ya zama silar da zai hana talaka fita filin zabe tunda tun kafin nazo duniya aketa fama a haka kakanin mu sun wahala iyayen mu sun wahala muma muna wahala kuma banga alamar da zata hana ‘ya’yanmu shan wannan wahalar a hannun mutanan nan ba, sai ikon ALLAH.

Duk lokacin dana tuna haka takaici yana isata nayi kokari ta hanyar da ALLAH ya nufe ni, nayi waka mai suna na gane duniya, nayi samari, kusa kusa akwai waka da nake cewa ‘yanci ya siyo raini a cikinta duk dan na haskawa mutane wasu abubuwa, amma na fahimci sakona baya zuwa inda nakeso ta bangaren nan zan kama baki na, babu wani abu da nake fata na samu al’umma su shiga damuwa a duniya, kuma bani da mai gida a siyasa dana taba kaiwa matsalata koda ta kwandala ce duk abunda ka ganni dashi daga ALLAH ne sai kuma masoya da baza su gogu a zuciyata ba.

Nayi alkawarin har siyasa ta huce bazan saka gunkin ko wanne dan takara a page dina ba, idan akwai wanda ya bani kudi domin nayi tallansa banyi ba ya kama ni, bana bukatar kudin sawa a aljihu makomar al’umma nake duba, amma nazarina ya kare ban hango mafita ba.

Don haka zan ja da baya na ci gaba da yin Addu’a ALLAH ya kawo mana mafita.

Kunji abinda mawakin yace sai kuyi nazari sosai domin wannan sakone.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: