Labarai

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano ya sauka daga shugabancin majalisar

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Honarabul Abdul’azeez Garba Gafasa da kuma shugaban masu rinjaye na majalisar Honarabul Kabiru Hassan Dashi, sun dangwarar da mukamin da su ke rike da shi a zauren majalisar.

Cikin wata sanarwar da Kakakin majalisar dokokin ya sanyawa hannu ya bayyana cewa ya yi hakan ne a bisa radin kan sa, sai dai shi kuma shugaban masu rinjayen bai bayyana dalilinsa na sauka ba.

Ana sa ran dai majalisar dokokin ta jihar Kano za ta zabi sababbin shugabannin a yau Talata, a wani zama da za ta yi.

#Kanomedia

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: